Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Sha Gaban Kasar Saudi Arabiya Wajen Samar Da Mai A Duniya, Inji.....


Wata rijiyar hakar mai.
Wata rijiyar hakar mai.
Majalisar mai hedkwata a birnin Paris ta fada cikin rahoton kiyasinta na shekara cewa Amurka tana kara tono danyen man fetur ta sabbin dabarun tsotso mai daga karkashin kasa.
Wata rijiyar mai a cikin teku.
Wata rijiyar mai a cikin teku.

Majalisar ta ce wannan karin danyen mai zai iya sa Amurka ta zamo mai dogaro da kai a fannin makamashi, daya daga cikin gurorin shugabannin Amurka.

Majalisar mai wakilcin kasashe 28 ta ce a yanzu Amurka tana sayen kashi 20 cikin 100 na man da take bukata daga kasashen waje ne. Amma nan da shekara ta 2030, nahiyar Arewacin Amurka zata zamo mai sayarda man fetur ga kasashen waje, kuma shekaru 5 bayan nan, Amurka zata zamo mai samar da dukkan man da take bukata a cikin gida.

Wannan hasashe wata sabuwar alkibla ce ga wannan majalisa wadda a can baya ta yi hasashen cewa kasar Sa’udiyya zata ci gaba da zama wadda ta fi kowa samar da man fetur a duniya har zuwa shekarar 2035.

A yanzu dai, Sa’udiyya tana samar da ganga miliyan 9 da dubu 800 a kowace rana, yayin da Amurka take samar da ganga miliyan 6 da dubu 700 a cikin gida a kowace rana.
XS
SM
MD
LG