Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa na Bikin Cikon Shekaru 235 Da Samun Mulkin Kai


Wani sabon samun takardar zama cikakken dana kasar Amurka, na kada tutar sabuwar kasar shi.
Wani sabon samun takardar zama cikakken dana kasar Amurka, na kada tutar sabuwar kasar shi.

Yau litinin rana ce ta bikin mulkin kai a Amurka

Yau litinin, rana ce ta bikin mulkin kai a nan Amurka, ranar hutun da mutane ke kira hudu ga watanYuli.

Albarkacin zagayowar ranar da iyayen kasa su ka ayyana mulkin kai daga Birtaniya a shekarar 1776, Amurkawa za su yi shagulgulan da za su hada da ciye-ciye a wuraren shakatawar da ke filin Allah, da pareti da kuma kade-kade da wake-wake.

Kamar yadda aka saba yi, da daddare za a yi wasannin wutad da za su haskake sararin samaniya a kananan garuruwa da manyan birane, kamar su Washington, DC, da New York da kuma Philadelphia inda aka rattabawa ayyanawar mulkin kai hannu.

Albarkacin ranar mulkin kan, za a yi bikin rantsar da mutum dari sabbin samun takardun zama ciakkun 'yan kasar Amurka a Mount Vernon a gidan shugaban kasar Amurka na farko,George Washington, a jahar Virginia, nan daf da Washington DC. Shugaban kasar mai ci yanzu kuma, Barack Obama, zai gayyaci sojoji da iyalan su, su je Fadar shi ta White House, su gasa nama sannan su kalli wasannin kade-kade da wake-wake.

XS
SM
MD
LG