Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Suna Matukar Bakin Cikin Kisan Da Aka Yi A Makaranta


Yan makaranta suna fita daga inda aka yi harbe harbe
Yan makaranta suna fita daga inda aka yi harbe harbe
Daruruwan masu makoki sun taru a majami’a a garin Newtown, jihar Connecticut jiya jumma’a da dare domin jimamin rashin kananan yara 20 da kuma wadansu mutane shida da wani dan bindiga ya kashe a wata makarantar firamare.

Hotunan talabijin sun nuna daruruwan masu makoki a waje bayan wadanda suke cikin majami’ar da ta cika makil, yayinda al’ummar ke binbinin bala’in da ya faru. Gwamna Dannel Maloy ya bayyana cewa, “mugun abu ya ziyarci wannan al’ummar yau”.

Tun farko a Washington, Shugaban Amurka Barack Obama cikin matukar bakin ciki yana kwalla, ya yi jawabi ga Amurkawa, inda ya bayyana jimamin rashin ya kuma ce tilas ne kasar ta dauki matakin kawo karshen irin wannan tashin hankalin.

Wannan kasa tamu ta fuskanci irin wannan masifa sau da dama a baya, ko a makarantar firamare ta Newtown, ko harbin kan mai uwa da wabi a jerin kantunan Oregon, ko a wurin ibada a Wisconsin, ko kuma a gidan silma a Aurora, ko a kan tituna dan birnin Chicago, wadannan duka unguwanninmu ne, kuma wadannan yaran, yaranmu ne. Kuma tilas ne mu hada kai mu dauki matakin hana ci gaba da aukuwar irin wannan bala’in, ko da menene ra’ayin siyasarmu.

Shaidu sun ce mutumin dan shekaru 20 da haihuwa sanye da bakaken tufafi da kuma rigar kare harsashe irin ta soja, ya shiga makarantar firamaren da safe ya budewa kananan yara wuta da malamansu a zuzuwa biyu. An sami wata bindiga irin ta sojoji a motarsa daga baya. Mutumin mai suna Adam Lanza ya kashe kansa, aka kuma sami wadansu kananan bindigogi biyu kusa da shi.

An gudanar da addu’oin tunawa da mamatan a birane da dama a duk fadin kasar.

Hukumomi sun ce, dan bindigar ya kashe mahaifiyarsa a gidanta kafin ya tuka motarsa zuwa makarantar.

Yan sanda basu tabbatar da masababin kashe kashen ba.
XS
SM
MD
LG