Zabar jihohin ya biyo bayan gasar shekara-shekara da gwamnoni suka kirkiro tsakanin jihohi da nufin karfafa maida hankali wajen yaki da cutar Polio.
Gidauniyar Bill Gates zata bada gudummuwar dala dubu dari biyar ga jihohin da suka lashe gasar, domin su iya shawo kan matsalolin da suka fi damunsu a fannin lafiya. Yana yiwuwa kuma su sami karin dala dubu dari biyu da hamsin sau biyu domin cimma burin kula da lafiyar al’umma.
Za a rabawa jihohin dalar Amirka miliyan daya domin su yi amfani dashi wajen gudanar da ayyuka jinya da kula da lafiyar al’umma saboda kokarin su a yaki da cutar ciwon inna.