Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Baiwa ‘Yan Achaba Da Masu Keke Napep Mako Hudu Suyi Rijista A Jihar Bauchi


Yan Achaba
Yan Achaba

Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa mutuwar masu sana'ar hayar Babura wanda ake kira da sunan Achaba, har guda 64 daga farkon shakarar nan yasa gwamnatin jihar yanzu ta tilasta yin rajista ga kowanne Dan Achaba, da kuma masu keke Napep domin shawo kan barazanar da masu sana'ar ke fuskanta a rayuwarsu.

Bincike dai ya nuna cewa baranar tsaron da jihohin Arewa maso Gabas suka fuskanta ala tilas yasa yawancin jihohin suka haramta sana’ar yin Achaba, bayan da aka hana ne a jihohin yasa masu yin Achaba suka ‘kaura zuwa jihar Bauchi inda ake ci gaba da sana’ar.

Sai dai kuma rahotanni kashe kashe da ake samu na ‘yan Achabar a watannin da suka gabata a jihar Bauchin kimanin guda 64, ya tilastawa gwamnatin jihar kaddamar da yin rijistar masu sana’ar yin Achabar da kuma keke Napep a jihar.

Shugaban kwamitin da aka damkawa wannan shiri, Air Commodore Tijjani Baba mai ritaya, yace akwai bata gari da ke kwararowa da wasu jihohi suna zuwa Bauchi domin yin wannan sana’a su kuma kawo rashin tsaro cikin ta. Kuma kwamitin ya bayar da wa’adin mako Hudu ga kowa da kowa yayi rijista.

Shima shugaban masu Achaba da keke Napep na jihar Abdullahi Mohammed Nabayi, yace yanzu haka yana da rahotan ‘yan Achaba har 64 da aka kashe, wasu an harbe su da bindiga, wasu kuma an caka musu wuka ko adda. Ya kuma kara da cewa akanyi dace a samu iyayensu wasu kuma ba a samu, haka yasa dole a binne su ba tare da sanin inda suka fito ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Mohammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG