Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kungiyar Tarayyar Afirka Na 27 A Kigali


Shugabannin kasashen Afirka
Shugabannin kasashen Afirka

An bude babban taro na 27 na Kungiyar Tarayyar Afirka ko KTA a Kigali, babban birnin Rwanda, inda a bana taken zaman shine “Shekarar Kare hakkin Bil Adama” musamman ma hakkokin mata. Shugabannin kasashen kuma zasu yi taron koli a ranakun 17 da 18 ga watan nan.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka shafi taron na bana shine cewar shugabar majalisar zartaswarta, Nkosana Dlamini-Zuma ta Afirka ta Kudu, ba zata nemi wa’adi na biyu kan wannan kujera ba.

Akwai rade-radin cewa kasashen Botswana, Equatorial Guinea da Uganda zasu mika sunayen ministocin harkokin wajensu a zaman masu neman wannan kujera.

Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kwamishan ta kungiyar tarayyar Afirka da zata sauka a taron
Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kwamishan ta kungiyar tarayyar Afirka da zata sauka a taron

Amma mawallafin wata jarida mai suna African Sun Times, kuma haifaffen Najeriya, Chika Onyeani, yace ya kamata a yi amfani da Dimokuradiyya a zaman zakaran gwajin dafi wajen zaben kasar da shugaban Tarayyar ta Afirka zai fito.

Yace bai kamata a kyautatawa shugabanni masu mulkin kama karya ta hanyar ba su kujerar shugabancin Tarayyar Afirka ba.

Onyeani yace ya kamata duk wanda zai gaji Dlamini-Zuma ya zamo mutumin da ya nuna abin koyi wajen mutunta tsarin mulkin kasarsa, musamman wajen mutunta ka’idar yawan wa’adin mulki, da yin zabe na gaskiya da kuma ba ‘yan adawa damar fadin albarkacin bakinsu a kafofin labarai.

Yace bai kamata a karrama Uganda da Equatorial Guinea ba a saboda shugabanninsu ‘yan kama karya ne.

XS
SM
MD
LG