Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Caccaki Murtala Nyako Tsohohon Gwamnan Adamawa


Tsohon gwamnan Adamawa Murtala Nyako
Tsohon gwamnan Adamawa Murtala Nyako

Wani rahoton bincike da aka fitar ya nuna jarirai dari hudu ke mutuwa daga kowane dubu daya da aka haifa a lokacin gwamnatin Murtala Nyako a jihar Adamawa

Rahoton da Farfasa Alubo da Dr Odetotinbo suka gabatar wurin bitar karawa juna ilimi ya nuna cikin jariri dubu daya da aka haifa a lokacin mulkin Murtala Nyako a jihar Adamawa dari hudu ke mutuwa.

Rashin ingantattun kayan aiki. magunguna da asibitoci suka jawo hakan. Masanan sun alakanta abun da ya faru a jihar da kasawar gwamnatin Nyako ta kebe wa fannin kiwon lafiya kashi goma sha biyar bisa dari na kason kudin jihar. Misali nera biliyan biyu da digo tara kacal aka kebewa fannin kiwon lafiya daga kasafin kudin 2014 a jihar dake da asibitoci 22 da likitoci 26 na nas 300 da sauran ma'aikatan kiwon lafiya 720.

Kungiyar da ake kira PAK da jami'ar Amurka dake Yola da kuma cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na jihar Adamawa sun caccaki matakin da tsohon gwamnan ya dauka na kashe biliyan shida wajen gina wani katafaren asibitin Jamus.

Sun bayyana ana iya anfani da kudaden wajen gyara asibitoci 22 da samarda ingantattun kayan aiki.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG