Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Fitaccen mai Fafutukar Kare Hakkin Bil adama a Kashmir


'Yan sandan India suna awon gaba da wani dan yankin Tibet
'Yan sandan India suna awon gaba da wani dan yankin Tibet

‘Yan sanda a yankin Kashmir na kasar India sun kama wani sanannen mai hankoron kare hakkin jama’a mai suna Khurram Parvez.

An cafke Parvez ne kwanaki biyu bayan an hana shi barin India domin ya halarci taron da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ke yi a Geneva kasar Switzerland.

Jami’an yan sanda ba su baiyana caje cajen da ake yiwa Mr Parvez ba.

A ranar Laraba hukumomin filin saukar jiragen sama, suka hana Mr Parvez shiga jirgi a birnin New Delhi zuwa Geneva inda aka shirya zai gabatar da rahoto.

Ana sa ran rahoton da zai gabatar a gaban jami’an Majalisar Dinkin Duniya zai kunshi bayanin zarge zargen tauye hakkin jama'a da ake yi a yankin Kashmir na kasar Indiya, inda tun watan Yuli yankin ke fama da hargitsi.

Yayin da yake zantawa da Muryar Amurka kafin a kama shi, Mr Pervez ya ce hukumomin filin saukar jiragen sama basu fada mishi dalilin hana shi shiga jirgi ba, illa kawai suka ce umarnin ne daga kungiyar leken asirin kasar.

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG