Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An ci gaba da gwabza kazamin fada jiya litinin domin neman mallakar Ras Lanuf


Jiragen yaki na kasar Libya sun kai hari ta sama.
Jiragen yaki na kasar Libya sun kai hari ta sama.

Sojoji masu biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya sun sake kai harin bama-bamai a rana ta biyu a jere a kan sansanonin ‘yan tawaye

Sojoji masu biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya sun sake kai harin bama-bamai a rana ta biyu a jere a kan sansanonin ‘yan tawayen dake kare wani birni mai muhimmanci a gabashin kasar. An ci gaba da gwabza kazamin fada jiya litinin domin neman mallakar Ras Lanuf inda ake da wata babba kuma muhimmiyar matatar mai. A ranar lahadi, mayaka masu gaba da Gaddafi sun janye suka komo wannan birni dake bakin teku daga garin Bin Jawad, a bayan da askarawan Gaddafi suka yi ta kai musu farmaki domin murkushe yunkurinsu na dosar Tripoli, babban birnin kasar. An ce wannan fadan ya dakatar da ayyukan mai a Ras Lanuf da kuma babbar tashar jigilar man fetur ta Brega dake kusa da nan, wuraren da tun kafin nan ba su aiki dari bisa dari. A yamma kuma, birnin Zawiya dake hannun ‘yan tawaye ya fuskanci farmaki mai muni a rana ta hudu a jere. An bada rahoton tsinke wayoyin tarho da na wutar lantarki da na sadarwar Internet, amma kuma wani kakakin ‘yan adawa da yayi magana ta wayar tarho ta tauraron dan Adam yace har yanzu sojoji masu gaba da Gaddafi suen suke rike da birnin. A wani labarin kuma, tsohon firayim ministan Libya, Jadallah al-Talhi, ya fito a gidan telebijin na kasar ya gayyaci shugabannin adawa da suka kafa cibiya a Benghazi da su zo a fara tattaunawa ta kasa baki daya. Mr. Talhi, wanda ya riek mukamin jakadan Libya a Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta dubu biyu da takwas, ya roki ‘yan tawayen da su yarda da tattaunawa domin a warware wannan rikici, a kawo karshen zub da jini, domin kuma kada a kyale ‘yan kasashen waje su sake kama kasar ta Libya. Wakilan majalisar mulkin da ‘yan tawayen suka kafa a Benghazi, sun yi watsi da wannan kiran su na masu fadin cewa ba zai yiwu a yi tattaunawar neman zaman lafiya ba sai fa idan Gaddafi ya sauka daga kan mulki.

Watch video of the events in Libya

XS
SM
MD
LG