Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjajjeniyar Wuccin Gadi Kan Shirin Nukiliyar Iran.


Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani

Manyan kasashen duniya shida da kasar Iran sun cimma ma wata yarjajjeniya, wadda ta kawo karshen shirin nukiliyar Iran da ake takaddama akai,

Manyan kasashen duniya shida da kasar Iran sun cimma ma wata yarjajjeniya, wadda ta kawo karshen shirin nukiliyar Iran da ake takaddama akai, akalla zuwa wani lokaci, sannan kuma ta kawo karshen takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba ma Iran.

Yarjajjeniyar mai wa’adin watanni shida, za ta bai wa masu tattaunwar lokacin tsara cikakkiyar mafita, game da ja-in-jar da aka yi shekaru 10 ana yi tsakanin Iran da Yammacin duniya kan shirinta na nukiliya.

Shugaban Amurka Barack Obama ya fadi da yammacin jiya Asabar a Washington cewa diflomasiyya ta bude wata sabuwar hanyar samar da duniya mai fiyayyar kariya.

Mr. Obama y ace idan Iran ba ta mutunta yarjajjeniyar sosai ba a yayin wa’adin na watanni shida, Amurka za ta janye saukin da ta samar mata sannan ta kuma tsananta matsin lambar.

Da yak e jawabi a birnin Geneva, Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry, ya ce babban burin wannan yarjajjeniyar shi ne a kai ga cikakkiyar maslaha da Irin. Amma kuma ya ce muhimman bangarorin takunkunan za su cigaba da aiki har zuwa karshen wa’adin na watanni shida masu zuwa.

Ministan Harkokin Wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya ce yarjajjeniyar wata dam ace ta kawo karshen dambarwar da ba ta da amfani. Y ace yarjajjeniyar har ilayau wata dam ace ta kawar da duk wasu shakku kan cewa shirin nukiliyar Iran kwata-kwata na zaman lafiya.

Dama abin da ya fi damun Amurka da mukarrabanta biyar – wato Rasha da China da Burtaniya da Faransa da Jamus shi ne batun inganta Yuraniyum, wanda za a iya amfani da shi a matsayin makamashin iza karfin nukiliya, amma kuma ana iya amfani da su a matsayin muhimman fannoni na bama baman nukiliya.

Manyan kasashen shida da su ka hada kai sun a so ne su kawo karshen ginawa da kuma girke na’urar inganta yuraniyum, a kuma dakatar da gina sabuwar tashar samar da sinadarin plutonium – wanda shi ma wani makamashi ne na bam din nukiliya.

Iran ta kuma yadda a rinka irin binciken da ba a yi a bay aba don tabbatar da cewa ta na mutunta yarjajjeniyar.
A madadin hakan, da Amurka da China da Rasha da Burtaniya da Faransa da Jamus za su yi sassauci da wuccin gadi ga Iran. To amma muhimman bangarorin takunkumin, kamar da mai da harkar banki da cinakayya za su cigaba da aiki.
XS
SM
MD
LG