Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cinna Wa Hedkwatar Ahmed Shafiq Wuta


Karir Madonna Sebagai Sutradara - VOA Career Day
Karir Madonna Sebagai Sutradara - VOA Career Day

Misrawa da suka fusata cewa tsohon firayim ministan na Hosni Mubarak zai shiga zagaye na biyu na zaben shugaba sun dira kan ofishinsa a al-Qahira suka yi kaca-kaca da wurin.

Misrawa masu zanga-zanga cike da fushin cewa firayim ministan karshe na hambararren shugaba Hosni Mubarak ya samu kaiwa ga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, sun dira kan hedkwatar yakin neman zabensa, suka yi kaca-kaca da ita, sannan suka cinna wuta a bayan da jami'an zabe suka tabbatar da sakamakon da aka bayar.

ma'aikatan gaggawa na Misra sun fada cikin daren litinin cewa sun kashe wutar da ta tashi a hedkwatar yakin neman zaben Ahmed Shafiq a birnin al-Qahira, kuma babu wanda ya ji rauni.

Tun da fari, wasu dubban Misrawa sun yi cincirindo a dandalin Tahrir na al-Qahira da wasu wurare a fadin kasar Misra su na rera taken nuna kin jinin sojoji da Shafiq da ma dan takarar jam'iyyar Ikhwanul Muslimun (Muslim Bortherhood), Mohammed Morsi.

Sakamakon zaben shugaban kasa na farko da aka gudanar cikin 'yanci a kasar ta Misra a makon jiya, ya nuna cewa Morsi na jam'iyyar Ikhwan shi ne a kan gaba, sai Ahmed Shafiq mai akidar tsame addini daga cikin harkar mulki yake biye masa a kusa.

Ana daukar Shafiq a zaman alama ko wakili na hambararriyar gwamnatin Mubarak, kuma takarar fitar da gwani a tsakaninsa da Morsi zata fi rarraba kawunan al'umma fiye da komai. Wannan sakamako ya raba kawunan Misrawa, ya kuma tunzurar da 'yan rajin da suka haddasa boren shekarar 2011 da aka yi wa gwamnatin Mubarak da 'yan mazan jiya da suka yi mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG