Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Taron Kolin Tarayyar Afirka A Habasha.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, a tsakiya, yake hanu da manyan jami'an tarayyar turai.
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, a tsakiya, yake hanu da manyan jami'an tarayyar turai.

An fara taron kolin kungiyar hada kan kasashen Afirka tareda kira ga wakilan kungiyar su dauki mataki na tunkarar fitinu da suke kunno kai a sassan nahiyar.

An fara taron kolin kungiyar hada kan kasashen Afirka tareda kira ga wakilan kungiyar su dauki mataki na tunkarar fitinu da suke kunno kai a sassan nahiyar.

Shugaban kungiyar Jean Ping yayi kira ga shugabanin kasashe dake nahiyar su dauki matakai na warware matsalolinsu da kansu.

Taron kolin zai maida hankali ne kan tsaro d a kuma cinikayya.

Tarayyar Afirka tace sai tayu ta tura sojoji domin yaki d a ‘yan tawaye da Jamhuriyar demokuradiyyar kwango. Haka kuma tana goyon bayan shirion kungiyar ECOWAS na tura dakaru domin zuwa Mali domin su yaki mayakan sakai a arewacin Mali masu da’awar Islama.

Haka taron kolin zai yi kokarin warware rikicin shugaban kungiyar.

Ping yana fuskantar kalubale daga minister harkokin cikin gida ta Afirka ta kudu Nkosazana Dlamini-Zuma. A karawar su ta farko a watan janairun bana babu daya cikin ‘yan takarar biyu da ya sami rinjaye na kshi 2/3 na kuri’u domin zama shugaba.

XS
SM
MD
LG