Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Yaki Da Cutar Sankaron Mama a Jihar Neja


Gwamna Ma'azu Babangida Aliyu na jihar Neja
Gwamna Ma'azu Babangida Aliyu na jihar Neja

An kaddamar da shirin wayar da kan jama’a akan cutar sankaron mama a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya.

Cutar sankaron mama na daya daga cikin cututtukan dake hallaka mata a duniya baki daya.

Dr. Muhammad Usman, darekta ne a matakin farko, a ma’aikatar lafiya a jihar Neja, yayi bayanin irin mutanen da wannan cuta ke saurin kamawa.

“Da farko mutum ya kasance mace, maza ma sukan samu, amma mata sunfi samun hatsarin wannan cuta. Na biyu macen da bata taba shayarwa ba, ko bata taba haihuwa ba. Sannan tsufa, ba’ace mata kanana baza su iya kamuwa ba. Mata masu jiki, da masu shan taba”, a cewar Dr. Usman.

Madam Aisha Muhammadu Wushishi, bayan kasancewa uwa, kuma jami’ar kiwon lafiya ce a jihar Neja.

“Wata wadda bata sani ba, baza ta san cewa yau tana da ciwon ba. Amma idan taje asibiti tace kamar tana jin wani abu da bai kamata ba, za’a duba ta, a ce mata ko shine, ko ba shi bane.

An raba na’u’rorin gwada cutar sankaron mama guda dubu hamsin da biyar kyauta ga jama’a, a kananan hukumomi ashirin da biyar dake fadin jihar Neja.

Za’a dauki dogon lokaci ana fadakarwa game da wannan cuta ta sankaron mama, a jihar Neja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG