Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Farfado Da Wani Shirin Rushe Gidajen Falasdinawa A Birnin Qudus


Hukumomin birnin Qudus sun farfado da shirin gina wurin shakatawa da cibiyar 'yan yawon shakatawa a wani wurin da za a rushe gidajen da Falasdinawa suka gina

Hukumomin birnin Qudus a Isra'ila sun amince da wani shiri na rushe gidaje kimanin 20 na Falasdinawa domin samar da wurin gina filin shakatawa da cibiyar masu yawon bude idanu da shakatawa a yankin gabashin birnin Qudus, inda akasarin wadanda ke zaune a ciki larabawa ne.

Litinin wata hukumar tsare-tsare ta birnin Qudus ta gabatar da wannan shiri na gina filin shakatawar da aka sanya ma sunan "King's Garden" a bayan da magajin gari Nir Barkat ya bukaci da su amince da wannan aikin ginin.

Har yanzu gina filin shakatawar yana bukatar karin izni, matakin da jami'ai suka ce zai dauki watanni.

A cikin watan Maris firayim minista Benjamin Netanyahu ya matsa lamba kan Barkat da a dakatar da wannan shirin gini a saboda damuwa kan yadda zai shafi martabar Isra'ila a idanun duniya.

Shugabannin Falasdinawa sun bayyana wannan aikin a zaman wani yunkurin dabam da Isra'ila ke yi na jaddada ikirarin ma;llakar dukkan birnin Qudus. Isra'ila ta ayyana dukkan birnin Qudus a zaman nata, bayan da ta kwace shi daga hannun Jordan a yakin 1967, amma kasashen duniya ba su amince da hakan ba.

XS
SM
MD
LG