Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fitar Da Afirka Ta Kudu Daga Gasar Cin Kofin Duniya


Kwallon Afirka ta Kudu na farko a ragar Faransa
Kwallon Afirka ta Kudu na farko a ragar Faransa

Duk da cewa ta doke Faransa a wasanta na karshe, Afirka ta Kudu ta zamo kasa mai daukar nauyin gasa ta farko da aka taba cirewa daga Kwallon Cin Kofin Duniya.

Afirka ta Kudu ta zamo kasar farko mai daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafar duniya da aka cire a zagayen farko, duk da cewa a wasanta na karshe yau talata a Bloemfontein ta doke Faransa da ci 2-1.

A daya wasan na rukunin farko ko "A" da aka buga, Uruguay ta doke Mexico da ci 1-0, abinda ya sa dukkansu biyu suka samu shigewa zuwa ga zagaye na biyu na kwaf-daya.

Luis Suarez ya jefa ma Uruguay kwallonta kwaya daya cikin minti na 43 da fara wasa lokacin da ya sa kai ya tura kwallon da Edinson Cavani ya bugo ta gefen ragar 'yan Mexico.

'Yan wasan Afirka ta Kudu Bongani Khumalo da Katlego Mphela sun jefa kwallaye biyu a ragar Faransa tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, a bayan da aka komo kuma sai dan wasan Faransa da ya shiga daga baya, Florent Malouda, ya rama kwallo guda.

Uruguay ita ce ta ke sama a rukunin na daya ko "A" da maki 7, sai Mexico da Afirka ta Kudu masu maki hurhudu, yayin da Faransa ta ke kashin baya da maki daya. Amma Mexico ce zata haye saboda yawan kwallayen da ta jefa araga sun fi na Afirka ta Kudu yawa.

Idan an jima, kungiyoyin dake rukuni na biyu ko "B" zasu kara, inda Najeriya zata hadu da Koriya ta Kudu a Durban, ita kuma Ajantina zata kara da Girka a Polokwane.

XS
SM
MD
LG