Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gagara Aiwatar da Kasafin Kudin Bana a Najeriya


Goodluck Jonathan yana jawavi ga wakilai a taron PDP na tsayar da dan takarar shugaban kasa a Abuja.
Goodluck Jonathan yana jawavi ga wakilai a taron PDP na tsayar da dan takarar shugaban kasa a Abuja.

Makonni biyu kennan, ana ta muhawara akan kasafin kudin bana, duk da cewa shugaba Goodluck Jonathan yayi rokon a aiwatar da shi a cikin gaggawa. Kuma bisa dukkan alamu, kawunan majalisar dattawan sun rarrabe akan kasafin kudin.

Senata Muhammadu Magoro, dan majalisar dattawa ne. Yace “wurin kasafin kudi, abinda ke damu na, wurin fanni kamar na sha’anin wuta, a gefen da na fito nake wakilta, babu wanda ya sadaukar da abinda ya gada kamar mutanen kasar Yawuri, saboda a lokacin da aka yi Kainji Dam, kusan kasafi daya a cikin hudu na kasar Yawuri, in nutsan da shi a cikin ruwa, don a baiwa Najeriyannan wuta. Yau mun wayi gari, an samu abinda ake cewa step down station, a nan Yawuri. Sai dai kuma a wannan shekara, ko sisin kobo ba’a saka a step down station din ba.”

A wata muhawa mai zafi, da yawanci ‘yan jam’iyyar adawa ta APC suka nuna rashin gamsuwarsu, ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki na goyon bayan dokar.

Ganin yadda muhawara ta kasance a majalisar ne yasa wakiliyar Muryar Amurka Madina Dauda ta tambaye Hadi Suleika daga jihar Katsina akan ko zasu iya bin umarnin jam’iyyar APC kuwa ganin cewa yanzu ba sune suke da rinjaye ba.

Hadi Suleika yace “babu ma yadda za’a yi a tattauna wannan kasafin kudi na bana, saboda akwai abubuwan da ba’a kawo ba, wadanda ya kamata a kawo su tare da kasafin kudi kamar abubuwan da suka jibanci yadda ake samo kudin ma su shigo Najeriya kafin a kasafa su, sai an fada. Da yadda za’a kashe kudin, da yadda za’a tsara su. Duk wannan sai an yi bayani filla filla tukunna kafin a kawo.”

Sai dai Abdulmumini Hassan PDP Jigawa yace ba zai yiwu a ce babu wani abu mai amfani a cikin kasafin kudin ba. Yace “Ina tabbatar da cewa, duk wadannan abubuwan, baka cewa an yi katon littafi irin wannan, wajen littatafai guda uku, kace babu komai wanda zai amfani mutane. Kawai abinda za’a iya cewa shine akwai wuraren da yakamata a ce an fi bawa muhimmanci, ba’a basu ba.”

A halin yanzu, majalisar dattawa ta mayar da kundin kasafin kudin ga kwamitin kula da kasafin kudi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG