Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Jirgin Da Ya Fadi A Kamaru Dauke Da 'Yan Australiya


Shugaban Kamaru, Paul Biya
Shugaban Kamaru, Paul Biya

Gwamnatin Kamaru ta ce an gano garwar jirgin saman da ya bace dauke da manyan 'yan kasuwa na kasar Australiya su 11, kuma babu alamar wani ya tsira da ransa.

Litinin din nan gwamnatin Kamaru ta ce masu binciken gaggawa sun gano garwar wani jirgin saman dake dauke da manyan 'yan kasuwa masu aikin hakar ma'adinai 'yan kasar Australiya. Jirgin ya bace a bayan da ya tashi daga Kamaru a kan hanyarsa ta zuwa Jamhuriyar Kwango.

Ba a samu ko da mutum guda da rai ba.

Wannan jirgi wanda wani kamfanin kasar Australiya mai suna Sundance Resources yayi hayarsa, ya bace tun ranar asabar, a lokacin da ya tashi daga Yaounde, babban birnin Kamaru, a kan hanyarsa ta zuwa Yangadou a cikin Jamhuriyar Kwango.

An tsinci garwar jirgin a cikin wani kurmin daji a cikin kasar Kwango.

A cikin jirgin akwai mutane 11, cikinsu har da daya daga cikin manyan attajirai na kasar Australiya, Ken Talbot.

Kamfanin Sundance yace shugaban kamfanin, Geoff Wedlock, da wasu manyan darektocinsa guda hudu su ma su na cikin wannan jirgin sama da ya fadi.

Kamfanin na Sundance yana bayyana kansa a zaman kamfanin hakar ma'adinai a kasashen Kamaru da Jamhuriyar Kwango. Babban aikin da kamfanin ke gudanarwa shi ne kamfanin hakar bakin karfe na Mbalam dake Kamaru, kamfanin da jaridun kasar Australiya suka ce yana iya samar da dubban miliyoyin daloli a tsawon rayuwarsa.

XS
SM
MD
LG