Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi Bakin Haure kan Zaben Najeriya


Wasu bakin Haure.
Wasu bakin Haure.

Zaben Najeriya bai shafe su ba saboda haka sun nisanci rumfunar zabe.

Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, mai kulla da jihar Jigawa Alhaji Isa Idris Jere, ya gargadi bakin haure cewa zaben dake tafe a Najeriya, bai shafe su ba saboda haka sun nisanci rumfunar zabe ko kuma su yabawa aya zaki.

Yayi wannan gargadi ne a wani taro da yayi da shuwagabanin bakin haure mazauna jihar Jigawa, yace gargadin ya zama wajibi ta la’akari da cewa a shekaran da ta gabata jami’an hukumar sun kama mutane ashirin ‘yan kasashen waje da katin hukumar zabe ta Najeriya.

Ya kara da cewa yanzu haka hukumar na tsare da wasu matasa ‘yan kasar Kamaru guda biyu da aka kama suna sayarda magunguna wani kamfani mai suna “Green World” ba tare da takardun izinin shiga kasa ba.

Alhaji Abdulrahaman Abdu, wanda yake shine shugaban alumar ‘yan Nijer, mazauna jihar Jigawa, shine ya jagoranci sauran bakin mazauna jihar , zuwa wajen taron.

Yace “duk bako wanda ba dan kasa bane ba hurumishi bane ya je ya shiga harkar zabe a wata kasa, mutanen mu sun koma su kalla suyi adu’a, don zaman lafiya, shine ya kawo mu, idan kasa babu zaman lafiya, muma ba zamu zauna ba.”

Gargadi ga BakinHaure - 3'04"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG