Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi ‘Yan Nigeriya Suje Domin Binciken Tarin Fuka


Wata mata mai fama da tarin fuka ta rufe baki da hanci
Wata mata mai fama da tarin fuka ta rufe baki da hanci

Shugaban cibiyar yaki da cutar fuka da ciwon kurkunu na jihar Kaduna Dr Julius Gajere, ya yi kira ga ‘yan Nigeriya su rika zuwa gwaji domin duba lafiyar jikinsu.

Shugaban cibiyar yaki da cutar fuka da ciwon kurkunu na jihar Kaduna Dr Julius Gajere, ya yi kira ga ‘yan Nigeriya su rika zuwa gwaji domin duba lafiyar jikinsu.

Dr. Gajere yayi wannan kiran ne a tattaunawa da ‘yan jaridu, a lokacin ganawa ta biyu a yunkurin yaki da tarin fuka a kananan hukumomi 23 na jihar.

Gajere yace akwai wurare 168 na bada magani da kuma dakunan bincike 63 a cikin jihar, ya kara da cewa shirin ya dauki masu wayar da kan al’umma akan cutar. Bisa ga cewarshi, cutar fuka tana da muni da kuma hadarin gaske saboda yadda take yaduwa cikin sauri kasancewa iska take yada ta ko’ina. Dr. Gajere kuma ya shawarci mutane suje duba kansu duk lokacin da suka kamu da tarin da ya wuce sati biyu. Yace gwajin, duba lafiya da yin magani ga tarin fuka kyauta ne, kuma ya gargadi ‘yan Nigeriya su yi amfani da wannan damar domin su san lafiyarsu.

Daya daga cikin masu gudanar da irin wannan binciken a jihar ya bayyana cewa, kalubalai da ake fuskanta a aiwatar da shirin sun hada da rashin kyaun hanyoyi da kuma rashin sa kai tsakanin al’umma na neman sanin ko suna dauke da cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG