Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar da Bukin Ranar Kutare a Jihar Maradi


Cutar kuturta
Cutar kuturta

Jihar Maradi ta jimhuriyar Nijar ta bi sahun sauran jihohi a kasar wajen gudanar da bukin ranar kutare ta duniya wadda ake yi a ranar 25 ga watan daya na kowacce shekara.

Jihar Maradi ta jimhuriyar Nijar ta bi sahun sauran jihohi a kasar wajen gudanar da bukin ranar kutare ta duniya wadda ake yi a ranar 25 ga watan daya na kowacce shekara.

Malam Idi Adamu, wani likita a Danja, a jamhuriyar Nijar yayi bayani kan alamun cutar kuturta. Ya bayanna cewa, alamun cutar kuturta dabam suke. Ya ce kuturta tana da tabbuna ga jiki amma banbancin tanbunan kuturta shine ba ya sa kaikayi.

Ya bayanna cewa alamomi kamar ciwon gwuiwa, rashin karfi ga hannu, ko kasala da faso a jikin mutum, sune ke tura mutum ya je wajen likita wanda zai iya ganowa cewa alamomin kuturta ne. Malam Adamu ya kuma ce ana bada maganin cutar kuturta a kyauta ne.

Sarkin kutare a jihar, Malam Salihu Musa ya ce suna neman taimakon gwamnati domin samun abinci.

Ga cikakken rahoton da Shuaibu Mani ya aiko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG