Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Gasar Tsere Kan Tsaunin Kamaru


A bana ma kamar sauran shekaru tun fara gasar tsere kan tsaunin kamaru mai tsawon mita dubu hudu, 'yan kasar mace da na miji ne suka suka zo na daya.

Duk da cewa kasar tana fama da rikicin siyasa tsakanin bangare mai magana da harshen turanci sarauniya da kuma masu magana da harshen Faransa, wanda ya faro daga zanga zangar da malamai da lauyoyi suka kira domin nuna rashin amincewarsu kan yadda da karfi da yaci sashen mai magana da harshen Faransa yake tauye musu a'adu da hakkokinsu.

Wannan batu yasa kungiyoyi masu ra'ayi kan batun suke bada shawarar a kafa jahar tarayya a bangarorin duka biyu a zaman hanyar warware wannan rikici, ko kuma baki daya a baiwa sashen mai magana d a harshen turancin Ingila 'yancin cin gashin kai.

Gasar ta bana mutane kalilan ne suka fito, watakil saboda kiran d a wasu kungiyoyi suka na kauracewa gasar.

Gasar na bana dan shekaru 32 da haifuwa Fai Elvis, daga yankin arewa maso yammaci, inda suke magana da turancin Ingila shine yazo na daya, ya kammala gasar cikin sa'o'i hudu da minti 25. Da saura mita dari 500 da kammala tseren ne ya tserewa wand a ya ci gasar a bara Gabsibium Godlove.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG