Sai dai kuma Majalisar koli ta malaman addini wadanda ke da alhakin tantance 'yan takarar ta yardar wa shugaban dake kan karaga a yanzu, Hassan Rouhani da ya tsaya takarar.
Rouhani mai sassaucin ra’ayi zai yi takara ne da biyu daga cikin fitattun masu tsatstsauran ra’ayi; Ebrahim Raisi wanda ake wa ganin mafi kusanci da shugaban addini Ayatollah Ali Khameni, da Magajin garin Tehran Mohammad Bagher Qalibaf.
Ahmadinejad ya ba da sanarwar tsayawar sa takara a makon da ya gabata a wani yunkuri na ban mamaki duk da shawarar da Khameini ya ba shi na cewa kada ya tsaya din.
Tsohon shugaban kasar wanda ake wa kallon mai ra’ayin rikau ko a cikin masu tsatstsauran ra’ayin, ya sauka daga mulki ne a shekarar 2013 bayan tangal-tangal da mulkinsa ya yi na raba 'yan kasar da kuma ke beta daga shauran kasashen duniya.
Facebook Forum