Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An jaddada mahimmancin koyon yin anfani da naurorin fasahar zamani


Dalibai a wata makarantar sakandare suna karatu da naurorin zamani
Dalibai a wata makarantar sakandare suna karatu da naurorin zamani

A yayinda ake gudanar da bikin ranar mata a Bauchi an jaddada mahimmancin koyon yin anfani da narorin fasahar zamani domin ko karatun boko yanzu baya tafiya daidai idan ba'a anfani da naurorin ana shiga yanar gizo domin tara bayanai

An gudanar da bikin ranar a Bauchi da suka hada da yiwa mata lacca da kuma baza kolin naurorin fasahar zamani kala kala.

Hajiya Maryam Maishanu shugaban cibiyar koyawa al'umma yin anfani da naurorin zamani a Bauchi ta yi bayani akan kokarin wayar da kawunan mata dangane da mahimmancin yin anfani da naurorin fasahar zamani.

Tace suna kokarin jawo hankalin mata akan mahimmancin koyo da yin anfani da naurorin zamani domin kusan yin komi yanzu ya ta'allaka ne akan samun ilimin naurorin zamani.

Shi ma Malam Isa Garba jami'in cibiyar nazarin zamani da cigaban al'umma. Yace yin anfani da naurorin zamani zai inganta rayuwar mata. Inda mata zasu mayarda hankali akan naurorin zamani al'umma zata fita daga takunkumin da take ciki, na rashin karfin tattalin arziki. Samun ilimin zai taimaki mata su daina dogara ga abun da maza suka samu kadai. Su yi anfani da naurorin su zama hanyoyin samun kudaden shiga.

Wasu mata da suka halarci taron sun bayyana yadda suke anfani da naurorin zamani. Suna yin karatu. Suna yin bincike cikin yanar gizo. Wata ma tace aikin makaranta baya yiwuwa sai da bincike ta yanar gizo.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye

Naurorin zamani
Naurorin zamani

XS
SM
MD
LG