Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Asibitin Maganin Cizon Maciji a Jihar Gombe


Maciji
Maciji

Gwamnatin jihar Gombe ta sa hannu a wani kwantaragi na Naira Miliyan 495 domin gina Asibiti mai gadaje 250 na maganin cizon maciji a karamar hukumar Kaltungo ta Jihar.

Gwamnatin jihar Gombe ta sa hannu a wani kwantaragi na Naira Miliyan 495 domin gina Asibiti mai gadaje 250 na maganin cizon maciji a karamar hukumar Kaltungo ta Jihar.

Yayinda yake magana lokacin bikin sa hannun wannan kwantaragin da aka yi a ma’aikatar lafiya tsakanin jihar da yan kwangila guda bakwai wadan da aka yarda da tayinsu, kwamishinan lafiya, Dr. Ishaya Kennedy ya baiyyana cewa babbar rana ce cikin tarihin ban a jihar kadai ba amma har da makwabtan jihohin wadan da ke da matsalar cizon maciji kuma suke dogaro ga asibitin domin samun magani.

A fadar sa, ginin asibitin, wanda zai dauki watanni 18 zai kasance da gadaje 250, wurin tara jini, dakin tiyata, wurin ajiye gawa da kuma katanga domin tsaro, da sauran su. Ya kara da cewa yayinda aka kamala wannan asibitin, zai rage cinkoson marasa lafiya a asibitin Kaltungo. Kwamishinan yace wannan cibiyar maganin cizon maciji kungiyar masu Bishara na Krista masu suna SIM ne suka kirkiro shi a shekara ta 1958 kuma ya tsara ta hannun gwamnatoci uku tun zamanin Jihar Arewa maso gabas.

Yayi bayanin cewa gwamnatin tarayya ta nuna sha’awarta na ganin ci gaban wannan wurin tun lokacin da amma ta kasa taka rawar gani domin tabbatar da hakan. Yace sakamakon marmarin da gwamnatin jiya take da shi a tallafawa majinyata, yanzu marasa lafiya, suna karbar magani da kwayoyi kyauta dalilin saboda tsadar magani wanda yafi karfin marasa karfi.

Yace cinkoson marasa lafiyan da ake samu a asibitin Kaltungo yana faruwa ne domin yawan marasa lafiyan dake gangarowa daga jiohin dake waje da jihohin dake sashen arewa maso gabas wadanda suke zuwa wannan cibiyar maganin macijin wanda kuma take yar kankanuwa. A bayanin sa na budewa, sakataren din din din na ma’aikatar lafiya, Dr. Saidu Garba yayi bayanin cewa kwantaragin ginin wannan asibitin ya fito ne sakamakon yawn koke koken cinkoson wandanda maciji ya sara dake fitowa daga asibitin Kaltungo.

Yayinda yake Magana a madadin yan kwangilan shida, Direkta gudanaswa na Consultech Nigeria Limited, Madam Dorin Wigwa ta tabbatarwa gwamnatin jiha cewa ba bin dokokin wannan dokar kawai zasu yi ba amma za suyi aiki ta hanyar da zasu bar gurbi ga sauran yan kwangila.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG