Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana fita a karamar hukumar Sardauna jihar Taraba


Wani mutum na wucewa ta kusa da motar 'yan sanda
Wani mutum na wucewa ta kusa da motar 'yan sanda

Shi dai wannan sabon tashin hankali ya auku ne biyo bayan yunkurin da wasu matasan kabilar Mambila suka yi na hana jami’an tsaron farin kaya, cafke wasu da ake zargin suna da hannu a tashe tashen hankula dake aukuwa a yankin.

.Kuma kamar yadda bayanai ke cewa wani dan siyasa a yankin ne yaje ya tunzura wasu matasa dake kusa da Nguroje don su hana kamun, kuma ganin basu samu sa’a ba, sai kawai suka shiga fashe fashe da kona taya har zuwa Gembu dake zama shedikwatar karamar hukumar Sardaunan.

Koda yake hukumomin tsaro basu tabbatar da batun asarar rayuka ba, wasu mazauna yankin da rikicin ya rutsa dasu sun bayyana cewa an kona gidaje baya ga rayukan da aka rasa ciki harda na dabbobi.

Wasu mazauna yankin da rikicin ya ratsu dasu, sun baiyaba hali da ake ciki da kuma iri hasarar da aka yi.

“ Mutane aMambila ne da Ngurori mutane sun yi ta gudu sai kuma wasu su ka zo domin su kwashe kayan su, aka yi ta kona gidan mutane. Shi kuma daya mutumin cewa yayi gaskiya a yankin mu abin ba kyau, wallahi ana kone gidajen mutane kuma an kashe wasu’’

Sun kuma yi bayanin cewa ba a kai jami’a tsaro ba har zuwa lokacin da wakilin sashen Hausa yayi magana da su. Haka kuma wani dan yankin yace akwai mutane 3 da ya tabbatar da mutuwar su

Tuni aka kafa dokar hana fita a wasu yankunan da lamarin ya auku baya ga tura karin jami’an tsaro da suka hada da sojoji kamar yadda ASP David Misal, kakakin rundunan yan sandan jihar Taraban ya tabbatar.

Ga karin bayanin wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdul Azeez.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG