Accessibility links

Iyalan Ba’amurkiyar nan ma’aikaciyar Jaridar Sunday Times of London Marie Colvin sun shigar da kara akan gwamnatin Syria, inda suke kukan cewa gwamnatin ta yi fako ne ta kuma kasheta a shekarar 2012.

Colvin ta mutu ne tare da wani dan jaridar daukar hoto Bafaranshe Remi Ochlik, lokacin da gwamnatin Bashar al-Assad ta yi dabarar harba makanin roka zuwa wani matsugunin ‘yan jaridu a birnin Homs da ke gundumar Bab Amr a ranar 12 ga Fabrairun 2012.

Har wasu ‘yan jarida 3 ma sun jikkata a wajen. Wata kungiyar rajin kare ‘yan jaridu a birnin New York tace, gwamantin Syria ta kashe su ne saboda kar su tona asirin kanshin mutuwar da aka yi aka kashe mutane a Homs.

Ministan yada labaran kasar Syria yace, a lokacin da abin ya faru, gwamnatin ba ta ma san Colvin da Ochlik suna kasar ba.

An dai shigar da wannan karar ne a madadin ‘yar uwar Marie da ake kira Cathleen Colvin da sauran iyalansu a shekaran jiya Asabar, a babbar kotun Amurka da ke nan birnin Washington DC.

XS
SM
MD
LG