Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Jihar Borno na Cikin Wahala


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima a Maiduguri, Mayu 22, 2014.
Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima a Maiduguri, Mayu 22, 2014.

Karancin Wutar lantarki ya jawo koma baya ga harkoki n masana'atu a jihar Borno

Rashin tsayayen wutar latarki ya jawo koma baya ga harkokin masana’antu a jihar Borno.
Shugaban ‘yan kasuwa da masana’antu na jihar Borno Alhaji Rijiya Bama, ne ya furta haka a hira dasuka yi da wakilin muryar Amurka Ibrahim Alfa Ahmed.

Yace “mutanen jihar Borno na cikin wahala,amma an barwa Allah yace har yanzu ana gudanar da harkokin kasuwanci a jihar,inda yace turawa ma suna zuwa suna tafiya,wannan garin harkar dake tafiya shine na Ridi da shanu.’

Ta bangaren masana’antu yace “yanzu ba zai yuba don ka san ba wuta koina ana harka da Diesel,Diesel gashi ya hau sama shi yasa,’yan Boko Haram basu suka kashe harkokin kasuwanci Borno ba wutar lantarki ne ya kashe,kullum muna Magana akan wutan duk Najeriya,amma namu yafi na wasu jihohi,shi ya kashe kasuwar Borno,daga baya kuma sai ‘yan Boko Haram, suka shiga amma har yanzu cikin garin Maiduguri a cike yake amma kasuwa ya kuma baya.”

Dangane da kasuwanci tsallaken iyaka kuwa Alhaji Rijiya Bama yayi nuni da cewa har yanzu ana kawo Ridi, daga Sudan da Chadi,amma bai kai kamar na da ba,kasan ana kashe-kashe da kuma tare hanyoyi ana kona kayan mutane shi yasa abun ya koma baya,amma duk da haka muna rokon Allah.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG