Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Matakan Tsaro A Fadar Shugaban Kasar Najeriya


Dakarun Sojojin Dake Tsaron Shugaban Najeriya
Dakarun Sojojin Dake Tsaron Shugaban Najeriya

Labarin kama wanda ake zargi Abdussalam Enesi Yunusa, da laifin aikin horas da yan Najeriya su shiga kungiyar ta’addanci ta ISIS da ‘yan Sandan Asiri DSS na Najeriya suka yi na nuna fadadar aikin ta’addanci fiye da Boko Haram a kasar.

Duk da ma labarin kama Yunusa wanda yake tsohon dalibi ne a jami’ar Kimiyya ta Minna ya faru ne tun tsakiyar watan jiya, yazo kuma dai dai da daukar karin matakan tsaro ga fadar shugaban Najeriya.

Takarda daga babban jami’in tsaron shugaban kasa Bashir Abubakar, ta umarci duk wani mai hulda da fadar ya tsaya a binciki motarsa yadda ya dace, da kaucewa al’adar wasu da kan wuce don su jami’an fadar ce ko kuma suna tuka wasu manyan mutane ne, don haka yazama wajibi daga yanzu duk wata mota mai duhun gilashi dole ne abude ta don ganin wanda ke ciki, a cewar sanarwar a irin wadannan motoci ‘yan ta’adda ke amfani wajen kai hari.

Kama Abdussalam Yunusa a Kano da labarin yace har ma ya fara tura wasu yan Najeriya Libiya, don karin samun horan ta’addanci, hakan bai zama abin mamaki ba ga wasu masana harkar tsaro.

Face an kai wanda ake zargin kotu, zai yi wuya a yanzu akara samun haske kan wannan labari, a tsarin jami’an tsaro na ganin labarai na shafar ayyukan bincikensu ne.

Ga Karin Bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG