Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Akalla Mutane 15 A Syria,A Farmaki Da Jami'an Tsaro Suka Kai Kan 'Yan Zanga Zanga


Tayoyi da masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati suke konawa,a da wasu shara kan tituna,bayan arangama d a jami'an tsaro.
Tayoyi da masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati suke konawa,a da wasu shara kan tituna,bayan arangama d a jami'an tsaro.

Masu hankoron kare hakkin jama’a a kasar Syria sunce an kashe akalla mutane goma sha biyar a jiya Laraba a birnin Daraa, ciki harda akalla mutane shidda wadanda aka kashe a lokacinda jami’an tsaro suka bude wuta akan masu zanga zangar kin jinin gwamnati kusa da Masallaci.

Masu hankoron kare hakkin jama’a a kasar Syria,sunce an kashe akalla mutane goma sha biyar a jiya Laraba a birnin Daraa, ciki harda akalla mutane shidda wadanda aka kashe a lokacinda jami’an tsaro suka bude wuta akan masu zanga zangar kin jinin gwamnati kusa da a kusa da Masallaci.

Shedun gani da ido sunce akwai akalla yaro daya a cikin wadanda aka kashe. Haka kuma an bada rahoto cewa jami’an tsaro sun kashe karin mutane a jiya Laraban.

To amma ita gwamnatin Syria cewa tayi mutane hudu ne aka kashe a tarzomar ta jiya Laraba. Kamfanin dilancin labarun kasar da ake cewa SANA ya bada labarin cewa mutane hudun da aka kashe a Daraa jami’an kiwon lafiya ne, wadanda yan banga dauke da makamai, suka kai musu hari.

A jiya Laraba ma’aikatar harkokin wajen Faransa tayi Allah wadai da tarzoma a Syria kuma tayi kira ga gwamnatin kasar data kaddamar da sauye sauyen harkokin siyasa.

A ranar talata shugaba Bashar al Assad ya kori gwamnan lardin Daraa. To amma korar gwamnan bata sa masu zanga zanga sun saduda ba.

XS
SM
MD
LG