Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe akalla mutane 72 a kasar Iraq


Majinyanci a asibiti a sakamakon hare haren da aka kai Iraqi Laraban nan akan masu ibada 'yan Shiya
Majinyanci a asibiti a sakamakon hare haren da aka kai Iraqi Laraban nan akan masu ibada 'yan Shiya

An kashe akalla mutane saba'in da biyu a hare haren da aka kai Iraq wadanda suka auna yan Shiya masu ibada.

An kashe akalla mutane 72 a hare haren da suka auna Musulmi yan Shiya wadanda suke ibada a Iraq, Kusan mutane maitan aka jiwa rauni a daya daga cikin rana mafi muni tun lokacinda sojojin Amirka suka janye daga kasar.

Yawancin bama baman da aka kai hare haren dasu, sun tashi ne a birnin Bagadaza da kuma biranen Jilla da Karbala da kuma Haswa a kudancin kasar wadannan yankunan da yan Shiya suka fi yawa wadanda yan tawaye yan Suni suka auna su a baya wajen kai hare hare.

Kusan mutane talatin suka mutu a lokacinda bama bamai guda hudu suka tashi ciki jerin gwanon masu ibada a birnin Bagadaza wadanda suke jerin gwanon tuna rasuwar Liman Moussa Al Kadhim, tattaba kunnen Annabi Mohammed Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A birnin Hilla kuma tashin bama bama da aka boye cikin wasu motoci guda biyu ne suka kashe akalla mutane ashirin da raunana kusan mutane arba'in. Wani bam cikin wata mota da aka ajiye kuma, ya tashi kusa da masu ibada a birnin Karbala mai tsarki ya kashe mutane biyu da raunana mutane ashirin da biyu.

Hare haren da aka kai sun faru a daidai lokacinda kasar Iraq ke fama da rikicin siyasa inda wakilan Majalisar dokoki, tsirarru yan Sunni da Kurdawa suke kokarin hambarar da gwamnatin Prime Minista Nouri Al Maliki, suna zarginsa da laifin nuna son kai domin ya baiwa yan Shiya iko da tasiri fiye da kima.

XS
SM
MD
LG