Accessibility links

Wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kashe jami'an 'yansanda biyu a lokuta dabam dabam yau a Maiduguri.

Saurari:

Da misalin karfe goma sha daya na safe agogon Najeriya, wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bindige wani jami'in 'yansandan ciki har lahira a unguwar Wange dake cikin Maiduguri. Jami'in ya gamu da ajalinsa ne yayinda yan bindigan suka zo su biyu a kan babur suka bude mashi wuta a kirji. Shaidu sun ce 'yan bindigan sun wuce kan babur kafin isowar jami'an tsaro wandanda suka isa wurin jim kadan bayan harbe shi, suka tarwatsa mutane suka tafi suka bar dan sandan a kwance jina-jina. Wadansu 'yan bindigan sun kuma bindige wani tsohon jami'in 'yansanda a Unguwar Bulunkutu dake cikin Maiduguri wanda shima yayi sanadin mutuwarsa nan take. Yanayin dake sa mutanen cikin Maiduguri da kewaye cikin wani tsoro da kuma zaman zullumi ganin yadda karin jami'an tsaro da kuma yawan binciken ababan hawa bai sa komi ya sauya ba.

XS
SM
MD
LG