Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Burma Fada Tsakanin Musulmi Da 'Yan Buddha Ya Halaka Mutane 67.


Hoton nan na wani musulmi ne a gaban tantinsa, inda aka tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu.
Hoton nan na wani musulmi ne a gaban tantinsa, inda aka tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu.
Fada na tsawon mako daya a kasar Burma, tsakanin mabiya addinin Budha na Rakhine, da musulmin da ake kira na Rohingya, ya raba mutane dubu 22 da muhallansu. Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a kasar ne ya bayyana haka.

Ashok Nigam, jami’in Majalisar a Rangoon, ya fada jiya lahadi cewa, kai tallafi ga wadanda suka tsere daga gidajensu zai kasance kalubale, domin wasu sunyi amfani da kwale-kwale suka gudu, wasu kuma sun nemi mafaka kan duwatsu dake can da nisa.

Ranar Asabar, gwamnatin Burma ta fada cewa an kashe mutane 67, aka kona gidaje dubu 2,800 sakamakon fadace fadacen cikin mako da ya wuce.

Kungiyar rajin kare hakkin Bil’-Adama mai cibiya a birnin New York, a sanarwa da ta bayar ranar Asaabar ta bayyana fargabar cewa sai tayu adadin wadanda ssuka halaka sakamakon rikicin, ya haura adadin da gwamnati ta bayar, saboda bayanai da wadanda suka stere daga fadan suka bayar, wadanda kungiyar tace musulmi ne suka fi tagayyara.
XS
SM
MD
LG