Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Dan Takarar Gwamna a Nijeriya


Rikice-rikice na kara tsanani a daidai lokacin da Nijeriya ke shirye-shiryen Zabe
Rikice-rikice na kara tsanani a daidai lokacin da Nijeriya ke shirye-shiryen Zabe

Yan sandan Nijeriya sun ce ‘yan bindiga dadi sun bindige wani fitaccen dan takarar gwamna da wasu mutane shida a jihar Borno ta arewacin Nijeriya.

‘Yan sandan Nijeriya sun ce ‘yan bindiga dadi sun bindige wani fitaccen dan takarar gwamna da wasu mutane shida a jihar Borno ta arewacin Nijeriya.

‘Yan sanda sun ce dan takara Modu Fannami Gubyo ya dawo daga sallar Jumma’a kenan a birnin Maiduguri sai wasu ‘yan bindiga dadi bisa Babura su ka harbe shi a harabar gidansa.

Gubyo dai dan takarar gwana a karkashin jam’iyyar “Nigeria People’s Party” (ANPP).

Ya zuwa lokacin harhada wannan labarin, babu wanda ya yi ikirarin kai harin, to amman wannan harin ya yi kama da irin harin da akan danganta shi da masu tsattsauran ra’ayin Musulunci na Boko Haram.

Ana ta samin karin tashe-tashen hankula a Nijeriya a daidai lokacin da ake dosar zaben da za a gudanar a watan Afirilu. ‘Yan sanda sun ce tashe-tashen hankulan da suka auku a yankin tsakiyar Nijeriya jiya Alhamis sun yi sanadin mutuwar mutane 12. ‘Yan sanda a jihar Filato sun ce wasu masu dauke da bindiga, da ake ganin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan akalla kauyuka uku.

Wani mai magana da yawun hukumar soji y ace sojoji sun kashe biyu daga cikin wadanda su ka kai harin a yayin das u ke kokarin tserewa. ‘Yan sanda sun ce sun damke a kalla 29 daga cikin wadanda su ka kai harin, ciki hard a wani jami’in ‘yan sanda da ke aiki a Abuja.

XS
SM
MD
LG