Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwance Bom a Owerri


Rundunar 'Yansandan Najeriya. (File Photo)
Rundunar 'Yansandan Najeriya. (File Photo)

An samu nasarar kaucewa tashin wani Bom a birnin Owerri dake Jihar Imo. Wakilin Sashen Hausa Lamido Abubakar, ya samu damar tattaunawa da kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Abdulmajid Muhammed.

“Larabannan da dare misalin karfe tara da rabi, muka samu labarin cewa an ajje wasu kamar jaka-jaka a wani gida inda ake sayar da abinci, ana kiran wajen, Kilimanjaro. Da muka gane Bom ne, sai muka kebe wuraren, muka hana mutane shiga. Wadanda suke wajen, muka kawar da su. Allah Ya bamu nasara, muka kwance abun kafin ya tashi.”

A halin yanzu dai jama’a a birnin Owerri sun koma wuraren da suke ayyukansu, babu wani tashin hankali. Kuma mun gargade su, ba masu cin abinci kadai ba, harda wuraren da ake shakatawa.

Speton na ‘yan sanda ya kara da cewa aikin tsaro, bana ‘yan sanda bane kawai. Kowa nada hannu, kuma idan aka tashi tsaye, to za’a ci nasara.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ake zargi da yunkurin shirin harin, amma rundunar ‘yan sandan na bincike.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG