Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kwantar da Nelson Mandela a asibiti


Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela
Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela

An kwantar da tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a wani asibiti dake birnin Johannesburg

An kwantar da tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela a wani asibiti dake birnin Johannesburg sakamakon ciwon mara da ya jima yana fama da shi.

Kakakin jam’iya mai mulki a Afrika ta kudu, Keith Khosa, yace an kai dan shekaru 93 fitaccen dan gwaggwarmayar yaki da wariyar launin fata asibiti ne, domin yi mashi wata jinya da shirya a lokutan baya, kuma babu wani abin damuwa.

Shugaba Jacob Zuma ya bayyana fatar alheri daga al’ummar Afrika ta Kudu ya kuma yi kira ga al’umma da kada a yiwa Mandela da iyalanshi shish-shigi.

Mr. Mandela wanda ya sami lambar yabo ta Nobel a shekara ta dubu da dari tara da casa’in da uku, baya fita bainin jama’a cikin watannin nan sabili da laulayi da yake fama da shi.

An daure Nelson Mandela na tsawon shekaru 27 kafin a sake shi a shekara ta dubu da dari tara da casa’in. Bayan shekaru hudu ya zama shugaban Afrika ta Kudu bakin fata na farko da ya kawo karshen mulkin wariyar launin fata.

XS
SM
MD
LG