Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Jami'ar Maiduguri Har Illa Masha Allahu


Wata motar da ta lalace kan wata hanya, a bayanda bam ya tashi a Maidugfuri, ranar 29 Yuni, 2011.
Wata motar da ta lalace kan wata hanya, a bayanda bam ya tashi a Maidugfuri, ranar 29 Yuni, 2011.

Hukumomin jami'ar sun dauki wannan matakin a bayan wasikar da suka ce sun samu ta barazanar farmaki daga kungiyar Boko Haram

An rufe wata jami’a dake arewacin Najeriya har sai illa ma sha Allahu, a bayan da jami’anta suka ce sun samu takardar barazana daga ‘yan Boko Haram. Jiya litinin aka rufe Jami’ar Maiduguri dake Jihar Borno, inda aka fi fama da wannan masifa, kuma jami’ai sun ce ba za a bude ba sai yanayin tsaro ya inganta.

Jami’ai suka ce jami’ar ta samu wasikar barazana daga kungiyar Boko Haram inda aka yi barazanar kai hari cikin jami’ar. Ana dora wa kungiyar Boko Haram alhakin kai wasu munanan hare-haren bam da farmakin da suka sa jama’a su na ta gudu daga garin Maiduguri a cikin ‘yan kwanakin nan.

An ce kungiyar ta ‘yan tsagera tana son kafa dokokin Musulunci masu tsauri a duk fadin arewacin Najeriya, ta kuma ki amincewa da tsarin mulki ko gwamnatin tarayyar Najeriya.

Akwai fargabar cewa wannan barazana ta Boko Haram tana yaduwa kudu zuwa Lagos. Wani sakon Text da aka ce wai kungiyar ce ta aika, ya gargadi mutane da kada su shiga motocin bas-bas na gwamnati domin za a kai musu farmaki.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa hukumomi sun bukaci fasinjoji da su sanya idanu sosai, su kuma bayar da hadin kai ga binciken kayayyakin da suke dauke da shi da za a rika yi.

XS
SM
MD
LG