Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Ma'aikatan Zabe A Arewacin Mali


Wasu mata su na talla kusa da fasta ta dan takarar shugaban kasa, Ibrahim Boubacar Keita, a Bamako, 16 Yuli, 2013.
Wasu mata su na talla kusa da fasta ta dan takarar shugaban kasa, Ibrahim Boubacar Keita, a Bamako, 16 Yuli, 2013.

Jami'ai suka ce ana tsammanin 'yan tawayen kabilar Abzinawa ne suka sace mutanen asabar daga garin Tessalit

Jami’ai a yankin arewacin Mali sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace mutane biyar, cikinsu har da jami’an zabe guda hudu, mako guda kafin zaben shugaban kasar da aka shirya da nufin maido da dimokuradiyya, zaman lafiya da hadin kai a wannan kasa.

Wani jami’in gwamnatin riko ta Mali yace ana kyautata zaton ‘yan bindigar ‘ya’yan kungiyar ‘yan awaren MNLA ce ta ‘yan kabilar Abzinawa, wadda ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnati a watan da ya shige.

An sace wadannan mutane ne jiya asabar a garin Tessalit.

Kungiyar MNLA ta kaddamar da yakin kafa ‘yantacciyar kasa ta Abzinawa a yankin arewacin Mali cikin watan Janairun 2012. A bayan da bijirarrun sojoji suka kifar da gwamnatin tarayya ta Mali a watan Maris, sai kungiyar ta MNLA tare da kungiyoyi masu alaka da al-Qa’ida suka samu nasarar kwace arewacin kasar.

Masu kishin Islamar sun kawar da ‘yan tawayen MNLA watanni kadan a bayan nan, kafin su kuma sojojin Faransa da na wasu kasashen Afirka su fatattake su daga yankin a wannan shekarar.
XS
SM
MD
LG