Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Wani Dan Kasuwa


'Yansanda na tsaro domin hana satar mutane
'Yansanda na tsaro domin hana satar mutane

A jihar Nejan Najeriya an sace wani attajirin dan kasuwa gap da fitowarsa daga masallaci bayan sallar isha'i

Wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba dauke da mayan bindigogi sun yi diran mikiya a kan wata anguwa da ake kira Kaduna Road a cikin yankin Suleja a jihar Neja inda suka yi awon gaba da wani attajirin dan kasuwa Alhaji Umaru Maikwarya.

Maharan da suka yi awon gaba da attajirin sun harbi mutum guda wanda tuni aka kaishi asibitin Gwagwalada inda yake karban magani. Lamarin da ya faru ranar Lahadi bayan sallar isha'i ya tayar da hankalin mutanen anguwar. Kawo wannan lokacin babu labarin inda aka nufa da wannan dan kasuwa.

Malam Mohammad Sani makwafcin Alhaji Umar Maikwarya ne ya ce wasu mutane ne suka biyo shi gida bayan ya yi sallar isha'i suka kama shi kana suka harba bindiga wadda ta samu wani bawan Allah dake kusa da wurin. Ya ce kawo lokacin da yake magana babu wani labari game da wanda aka sacen. Lamarin, inji shi, ya faru ne misalin karfe bakwai da rabi.

An kaima jami'an tsaro rahoton abun da ya faru. Don haka ita ma rudunar 'yansandan jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin. Kakakin 'yansandan Mr. Richard Adamu ya ce sun samu rahoto amma basu da wani labari har yanzu. Ya ce an fada masa an kinkimoshi an sashi a mota amma babu wanda zai ce ga irin motar ko launinta ko dai yadda ta ke. Sai dai rundunar ta ce tana kan maganar domin satar mutane a Najeriya ya zama ruwan dare gama gari.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG