Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Roki Al'ummar Kano Da Su Rungumi Yaki Da Polio


A bayan da aka samu wata matsala a yankin Tarauni, an roki al'ummar Jihar Kano da kada su yarda da masu yada jita-jitar cewa maganin rigakafin Polio ya lalace

An janyo hankalin al'ummar Jihar Kano da su yi banza da jita-jita maras tushe da wasu ke yadawa cewa maganin da aka kai jihar domin digawa yara a zaman rigakafin cutar Polio ya lalace.

Da yake karbar wani rahoto kan wannan aiki a yankin karamar hukumar Tarauni, jagoran kwamitin yaki da cutar Polio a Jihar Kano, kuma mataimakin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace ba za su zuba ido kawai su koma gefe su na kyale ma'aikatan da aka dora wa amanar gudanar da aikin su na yin abinda suka ga dama.

Yana magana ne kan yadda aka bar wasu na'urorin sanyaya maganin, watau Firij, babu wuta jikinsu a Tarauni, alhalin da wannan magani yake bukatar a koyaushe a bar shi cikin sanyi. Sai dai Dr. Ganduje yace wannan bai kai ga lalacewar maganin ba.

Wakiliyarmu ta kiwon lafiya, Baraka Bashir, ta aiko da cikakken bayani kan wannan lamari daga Kano...
Gwamnatin Kano Ta Bukaci Jama'a Su Goyi Bayan Yaki Da Polio - 2:22
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG