A yau Juma’a sakataren harakokin wajen Biritaniya, Philip Hammond ya tabattar da cewa an sako Shaker Aamer, wanda asalinsa dan kasar Sa’udiyya ne.
Kuma a yau din ake sa ran Aamer zai isa Ingila.
Tun shekarar 2002 aka tsare shi a wannan gidan kason ba tare da an tuhumce shi da wani laifi ba, kuma ba a gabatar da shi a gaban wata kotu ba.
An soma tsare shi ne a kasar Afghanistan a shekarar 2011 bayan da aka zarge shi da cewa ya yi jagorancin wata kungiyar mayaka ta Taliban kuma wai har ya taba saduwa da madugun al-Qaida, Osama Bin Laden.
To amma Aamer ya musanta zargin, ya ce ya je ne Afghanistan da iyalinsa don gudanar da aikin ba da jin kai.