Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samarma Mata Sama Da Dari Hudu Aikin YI


Mata da yara
Mata da yara

A wani mataki na rage zaman banza tsakanin mata da matasa matar gwamnan jihar Gombe ta ce ta samarma mata fiye da dari huduaikin yi cikin shekaru biyu

A kokarin da gwamnatoci da wasu hukumomi keyi domin rage barace-barace da zaman kashe wando da wasu matsaloli da mata ke fuskanta uwargidan gwamnan jihar Gombe Hajiya Adama Ibrahim Hassan Dankwambo ta yi ikirarin samarma mata sama da dubu hudu sana'o'i daban daban cikin shekaru biyu.

Ita ma gwamnatin Gombe ta yi alkawarin taimakawa matar gwamnan da kokarinta na inganta rayuwar mata. Gwamnan jihar ne ya fadi hakan yayin bikin yaye shirin horas da mata kashi na bakwai. Ya ce ya ga yadda shirin ya baiwa mutane dubu hudu aiki kai tsaye. Idan kuma an yi la'akari da wadanda zasu ci gajiyar dubu hudun ana iya cewa mutane fiye da dubu goma sha shida suka samu abun yi. Ya ce suna goyon baya kuma zasu yi duk abun da ya cancanta dpmin a cigaba.

Matar gwamnan ta kira mata su kula da tarbiyar yara da mazajensu. Su tabbatar yara sun je makaranta domin rashin karatun ne ya cuci wasu. Ta ce dan taimakon da aka samu a zauna gida kada a soma gantali a gari ana yin batanci.

Malam Hassan Adamu mai baiwa matar gwamnan shawara kan ayyuka na musamman ya roki mata da basa cikin talauci su dena kutsa kai wurin neman dole sai an raba kayan taimakon da su. Wadanda suka fi karfin dubu hamsin bai kamata su mayar da kansu baya ba. Su bari a taimaki wadanda basu da karfi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG