Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami ingancin samar da wutar lantarki a Najeriya


Wani ma'aikacin wutar lantarki
Wani ma'aikacin wutar lantarki
Mazauna wadansu jihohin Najeriya sun bayyana cewa, an fara samun inganci a yunkurin gwamnati na samar da wutar lantarki duk da yake har yanzu ana fuskantar dauke wuta a sassa da dama na kasar.
Wakilan Sashen Hausa na Muryar Amurka a jihohin Kano da Sokoto sun zaga wadansu unguwanni da kuma wuraren kasuwanci da aka fi amfani da wutar lantarki domin tantance harsashen da ministan makamashi na Najeriya Farfesa Bart Njaji ya yi, inda ya bayyana cewa an iya samar da karfin megawatt na wuta 4,237 a halin yanzu.
Wadanda wakilan namu suka zanta dasu a jihohin biyu sun bayyana gamsuwa da ci gaba da aka samu suka, da kuma fatar ba shigo shigo ba zurfi kamfanin kasar Canada da aka ba aikin gudanar da harkokin wuta yake yi ba daga baya a koma gidan jiya.
Kafin wannnan lokacin dai bisa ga cewarsu, wadansu sassan jihar basu ganin haske wuta na tsawon kwanaki, yayinda ake dauke wutar bayan sa’oi wadansu lokutan ma kasa da haka bayan kawo ta.
XS
SM
MD
LG