Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sassauta Dokar Takaita Zirga Zirga a Borno


'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da sassauta dokar hana zirga zirga a jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe bakwai na maraice, sabanin yadda yake a da, daga karfe shida zuwa karfe goma na dare, domin jama'a su sami walwala a ranar damokaradiya.

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da sassauta dokar hana zirga zirga a jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe bakwai na maraice, sabanin yadda yake a da, daga karfe shida zuwa karfe goma na dare.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Dr. Mohammed Bulama ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai inda ya bayyana irin shirye shiryen da ake yi na bukin ranar Damokaradiya a jihar.

Kwamishinan yace gwamnati tana kuma shirin gudanar da wadansu shirye shirye na tunawa da zagayowar wannan rana da ya hada da liyafa ga ‘yan siyasa, da kuma wasan kwallon kafa. domin tunawa da wannan ranar.

An dage dokar takaita zirga zirgar ne domin jama’a su sami sukunin gudanarda bukukuwan. Kwamishinan yace kananan yara kusan miliyan daya ne ke gudun hijira a Maiduguri, ya kuma ce al’ummar jihar sun hakikanta cewa gwamnatin Muhammadu Buhari zata taimaka wajen shawo kan matsalar.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana.

Shirin Ranar Damokaradiya a Borno - 2'51"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG