Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sassauto Da Dokar Hana Fita A Wasu Unguwannin Maiduguri


Wasu mata na wucewa a wata unguwa cikin Maiduguri, inda ake aiki da dokar ta baci, Lahadi 19 Mayu, 2013
Wasu mata na wucewa a wata unguwa cikin Maiduguri, inda ake aiki da dokar ta baci, Lahadi 19 Mayu, 2013

An sassauto da dokar hana fita waje, a wasu unguwanni 12 na Maiduguri, ya koma daga 5 na yamma zuwa 7 na safiya.

Al’ummar jihohi uku a arewa maso gabashin Najeriya da Shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kakaba ma dokar ta baci makon da ya gabata sun samu kansu a wani halin tsaka mai wuya.

A garin Maiduguri ran Asabar, sojoji sun kafa dokar takaita zirga-zirga na sa’o’i ashirin da hudu a wasu unguwanni goma sha biyu. Sai jiya sojojin suka dan yi sassauci.

Bisa ga sanarwar da sojoji suka fitar mutane na iya fita daga karfe bakwai na safe zuwa karfe biyar na yamma. Wannan lamarin ya shafi harkokin kasuwanci da na yau da kullum.

Masu sayar da katin salula sun koka da dokar. Wani da aka zanta da shi yace kafin dokar ya kan sayar da kati na kusan nera dubu talatin ko fiye ma. Sai yau an wayi gari ko sisin kwabo baya samu. Bugu da kari ita kafar salula din hukumomi sun rufeta bayan an yi shekaru goma ana anfani da wayar salula.

Makarantu ma basu tsira ba. Wani da aka zanta da shi yace tun da aka kafa dokar makarantu suke rufe sai ranar Laraba da ya kai dansa da safe amma karfe goma sha daya na yi aka kirawo shi ya dauki dansa. Masu aikin sufuri su ma sun samu cikkas. Babu wurin anfani da hanayar sadarwar yanar gizo sai mutane sun bi dogon layi a gidan gwamnati.

Ga rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Biu ya aiko domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG