Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tantance Mahara Biyu da Suka Kai Farmaki a Jihar California


Hukumomin birnin San Bernardino na jihar California da ke nan Amurka sun tantace sunayen mutane biyun da suka kai wani farmaki da bindigogi jiya akan wata cibiyar kula da masu fama da nakassa, inda har mutane 14 suka rasa rayukkansu, wasu 17 suka jikkata.

Mutanen biyu da babban sufeton ‘yansandan garin Bernardino, Jarrod Burguan ya bayyana sun hada da Syed Farook, dan shekaru ashirin da takwas da haihuwa, wanda haifaffen Amurka ne da kuma wata mace mai suna Tashfeen Malik, 'yar shekaru 27 da haihuwa.

Sufeton ‘yansandan ya ce mai yiyuwa ne mutumin da matar, ko dai mata da miji ne ko kuma suna shirin suyi aure. Kafofin watsa labarai biyu da suka hada da kampanin dillacin labaran AP da jaridar Los Angeles Times duk sunce Syed da Tashfeen mata da miji ne, har ma sun taba haihuwa.

Mr. Burguan ya ce shi Farook ma’aikacin sashen kula da lafiya na karamar hukumar mulkin San Bernardino ne a da, a lokacin da abin ya faru ana cikin shiryawa cibiyar kula da nakasassun liyafar kirsimeti. An ce Farook ya bar wurin da ake wannan shirin ne a fusace, ya je ya dawo da ita Tashfeen, kowannesu dauke da tarin bindigogi da albarussai iri-iri.

Daga baya jami'an tsaro suka gano Farook da Malik a wani gida a garin Redlands kusa da inda aka kai farmaki. An yi musayar wuta tsakanin 'yansanda da maharan wadda ta yi sanadiyar kashe Farook da Malik yayinda 'yan sanda ke bin su a mota. Dan sanda daya ya sami rauni amma ba mai barazana ga rayuwa ba ne.

Labarai masu alaka

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG