Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yanke wa wani Malamin addinin Musulunci hukuncin daurin rai da rai a Amirka


Abu Hamza
Abu Hamza

Alkali wata kotun taraiyar a birnin New York, Amirka ya yanke wani mai wa'azin addinin Musulunci mai una Abu Hamza daurin rai da rai.

Alkalin wata kotun taraiyar a birnin New York nan Amirka ya yankewa wani mai wa'azin addinin Musuunci daurin rai da rai a gidan yari, watani takwas bayan da aka same shi da laifin caje cajen ta'adanci da aka yi masa.
Jiya Juma'a alkali ya yankewa Mustafa Kamel Mustapha wanda aka fi sani da sunan Abu Hamza hukuncin a wata kotun taraiyar dake birnin New York.
Abu Hamza wanda, idonsa daya ne, kuma an yanke dukkan hanayensa yana kotu a lokacinda aka yanke masa wannan hukunci. Lauyan dake kare shi ya roki alkali daya la'akari da halin da shu Abu Hamza yake ciki na rashin ido daya da hanaye biyu kafin ya yanke masa hukuncin.
A watan Mayun bara aka samu Abu Hamza da aikata dukkan laifuffuka goma sha daya da ake zarginsa da aikatawa, na baiwa yan ta'ada kayayyakin aiki. Sun hada harda tura magoya bayansa samun horo a sansanoni yan jihadi anan Amirka da tura maza taimakon kungiyar Al Qaida a Afghanistan da baiwa yan yakin sa kan kasar Yamal wayoyin satelite da kuma sace turawa yan yawon bude ido a alif dari tara da casa'in da takwas.
Yan yawon bude ido hudu ne suka mutu a lokacinda aka yi kokarin ceton su.
A wata sanarwar daya gabatar a jiya Juma'a, atoni Janaral na Amirka John Calin ya baiyana Abu Hamza a zaman dan ta'ada na kin karawa wanda ba zai tuba ba.

XS
SM
MD
LG