Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yankewa wadanda suka lakadawa shugaban kasar Mali duka hukumcin dauri


Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Mali Dioncounda Traore, a hagu
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Mali Dioncounda Traore, a hagu
An yanke hukumcin daurin watanni shida-shida a kan mutane 6 da aka samu da laifin lakkada ma shugaban rikon kwarya na kasar Mali duka a cikin ofishinsa.

A yau laraba wani alkali ya samu mutanen 6 da laifi ya kuma yanke musu wannan hukumci a Bamako, babban birnin kasar.

Mutanen su na cikin gungun mutanen da suka kutsa cikin ofishin shugaban rikon kwarya Dioncounda Traore a ranar 21 ga watan Mayu, suka lakkada masa duka har sai da ya suma. An kai Mr. Traore zuwa kasar Farans ainda yayi watanni biyu yana jinya.

Mazauna birnin Bamako da suka yi magana da Muryar Amurka sun ce wannan hukumci yayi kadan, amma dai sun gamsu cewar an yi hukumci kan lamarin.

Hukumomi sun ce mutanen da suka kai hari kan shugaban rikon kwaryar magoya bayan juyin mulkin da aka yi ranar 22 ga watan Maris ne karkashin jagorancin Kyaftin Amadou Sanogo.

Madugun juyin mulkin ya mika wuya ga matsin lambar kasashen duniya ya yarda aka kafa gwamnatin rikon kwarya da zata maida kasar bisa turbar mulkin farar hula.
XS
SM
MD
LG