Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gangamin Fadakar da Jama'a kan Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Filato


Masu kada kuri'a a Najeriya a rumfar zabe.
Masu kada kuri'a a Najeriya a rumfar zabe.

Ma'aikatar yada labarai ta jihar Filato ta shirya gangamin fadakar da jama'a game da zaben kananan hukumomi da za'a yi kusan karshen wannan watan

Gwamnatin jihar Filato ta yi anfani da ma'aikatar watsa labarai ta shirya gangamin fadakar da jama'a dangane da zaben kananan hukumomi da za'a yi a jihar ranar 25 ga wannan watan.

Jama'ar Filato sun bukaci gwamnatin jihar da ta tabbatar da tsaro yayin gudanar da zaben kananan hukumomi. A gangamin da ma'aikatar watsa labarai ta gudanar a karamar hukumar Bassa masu ruwa da tsaki kan harkar zaben sun bayyana takaicinsu kan matsalolin tsaro musamman a rumfunan zabe lamarin da kan jawo hatsaniya da tashin hankali.

Mr Richard Adamson wanda ya wakilci al'ummar hukumar a wurin taron ya yi korafi kan rashin kawo kayan zabe kan lokaci. Yace da an soma kuma za'a ce lokaci ya kure sai a dakatar da mutane duk da wai suna kan layi suna jira su kada kuri'unsu. Wani abu kuma da ya tabo shi ne batun wadanda katinsu ya bata. Yace "Da so samu ne sai a displaying sunayen mutane kafin ranar zaben"

Basaraken gargajiya Ogon na Pengana Da Isaac Sambo yace "Gudunmawarmu kamar sarakuna zamu roki talakawanmu su bi in good order. Ban da fada, A yi zabe lafiya. Kada a kawo rigima a cikin zabe.Kuma muna ba gwamnati shawara cewa duka wanda ya ci zabe a bashi hakinsa".

Jami'in zabe na hukumar Bassa Tagyer Silas yace za'a gudanar da zaben ranar ishirin da biyar na wannan watan. Ranar zaben za'a fara tantance sunaye daga karfe takwas kana a daina a karfe uku amma zaben zai cigaba. Dangane da korafin cewa wasu suna sayen katin zabe ko me jami'in zai ce a kai. Sai yace "In ka zo zamu checking sunanka da wannan katin da ka kawo" Wato sunan mutumin ya kasance shi ne a katin da kuma hotonsa. Idan katin da mutum ya kawo ba nashi ba ne to "akwai hukunci maitsanani".

Mr. Danladi Daniel ya bayyana muhimmancin yin adalci a zaben. Yace "Mu dai Allah muke dubawa. Ba wani adalci da za'a yi a wannan zaben.An riga an gama zabe. In kin lura akwai wadanda ke da damuwoyi cikin party amma har yanzu party ta mika masu flag don su yi contesting election da za'a yi. Ya nuna cewa babu wani adalci da za'a yi. Mu kawai mun rungumi kaddara muna jiran abun da Allah zai yi"

Amma kwamishanar yada labarai ta jihar Madam Olivia Dazem tace gwamnati bata da niyyar dora kowa kan mukami sai wanda ya ci zabe. Ta ce abun da gwamnati ke bukata shi ne bin doka da oda domin a yi zabe cikin lumana.Ta gargadi iyaye su fada ma 'ya'yansu kada su bari a rudesu da kudi domin su tada hankali.

Shugabannin addini ma sun yi magana kan zaman lafiya.Pasto Ado Bukas sakataren kungiyar kiristoci reshen Bassa yace basa fatan rikici. Zancen addini kuma bai kamata ya taso ba a siyasa. Shi ma Mohammed Tahiru limamin Bassa ya ce gudunmawarsu bata wuce su ce a zauna lafiya ba domin idan babu zaman lafiya addini ma ba zai yiwu ba.

Za'a yi zabukan amma banda kananan hukumomin Jos ta Kudu da Wase bisaga abun da gwamnati ta ce sabili da dalilan tsaro.Sai nan gaba za'a yi nasu
XS
SM
MD
LG