Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Garkuwa Da Wasu Mutane A Nijeriya


Masu garkuwa da mutane a Nijeriya kan boye fuskokinsu don kar a gane su.
Masu garkuwa da mutane a Nijeriya kan boye fuskokinsu don kar a gane su.

Kafafen yada labaran Nijeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mata, da diya da kuma direban wani alkalin kotun koli

Kafafen yada labaran Nijeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mata, da diya da kuma direban wani alkalin kotun koli, a al’amari na baya-bayan nan na auna fitattun ‘yan Nijeriya da masu garkuwa da mutane ke yi.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito hukumomi na cewa an sace mutanen ne da yammacin ranar Jumma’a a jihar Edo ta kudancin kasar. Jami’an sun ce mutane ukun na hanyarsu ta zuwa Benin, hedikwatar jihar Edo don shirye-shiryen auren diyar alkalin yayin da ‘yan bindigar su ka tsaida motarsu.

Rahotannin sun ce wadanda suka sace mutanen ba su tuntubi iyalin Alkalin Kotun Koli Bode Rhodes-Vivour don gabatar da wata bukata ba.

Sace-sacen fitattun mutane sun karu a kudancin Nijeriya a ‘yan watannin nan, ta yadda akasarin lokaci masu sace mutanen kan bukaci kudaden fansa daga iyalan mutanen da su ka sacen.

A watan Disamba ma, an sace mahaifiyar Ministar Kudin Nijeriya Ngozi Okonjo-Iweala a jihar Delta kafin aka sako ta bayan kwanaki 5. Ba a bayyana ko an biya kudin fansa ba.

Garkuwa da mutane dai ta zama sana’a mai kawo kudi sosai ga bitsararru a kudancin Nijeriya, to amma a shekarun da su ka gabata, akasarin al’amarin na shafar ‘yan kasashen waje ne da ke aiki da kamfanonin mai.
XS
SM
MD
LG