Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jinyar Wani Rukunin Masu Fama Da Cutar Kanjamau A Faransa


Ana gwaje-gwajen maganin kashe cutar HIV
Ana gwaje-gwajen maganin kashe cutar HIV
Wasu mutane dake dauke da kwayar cutar HIV a kasar Faransa sun ci gaba da rayuwa lafiya kalau bayanda suka daina shan maganin da yake kashe kaifin cutar. Dukan mutanen sun fara shan maganin ne cikin makonni goma da tabbatar da kamuwa da cutar.

An gudanar da binciken ne a kan wadansu mutane 14 da ake kira da turanci “Visconti chohort”, mutanen sun ci gaba da shan maganin na tsawon shekaru uku tun daga lokacin da suka fara shan magani cikin makonni goma da kamuwa da cutar.

Binciken ya bayyana cewa, sanin mutum yana dauke da cuta cikin lokaci da kuma fara jinya ba tare da bata lokaci ba zai taimaki a kalla mutum daya cikin goma da suka kamu da cutar kanjamau ya warke, inda ake kashe kaifin kwayar cutar duk da yake tana nan, amma mutum zai iya ci gaba da rayuwa ba tare da shan maganin ba.

Mutanen goma sha hudu da aka gudanar da binciken a kansu yanzu sun yi shekaru bakwai da daina shan magani kuma suna cikin koshin lafiya.

A farkon wannan watan ne jami’an kimiyya a Amurka suka sanar da cewa sun warkar da wata jaririya da aka Haifa da kwayar cutar HIV bayan an fara bata maganin kashe kaifin kwayar cutar cikin sa’oi 30 da haihuwarta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG